(ABNA24.com)Babban kwamandan dakarun kare juyin Musulunci na Iran (IRGC), Manjo Janar Hossein Salami ya ce kasashen yankin Tekun Fasha ne kawai za su iya tabbatar da tsaron yanki ba wasu kasashe daga waje ba.
Manjo Janar Salami ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a yammacin jiya Alhamis a garin Mashhad mai tsarki inda ya ce babu wata kasa ko hadakar kasashen waje da za su iya tabbatar da zaman lafiya da tsaron yankin Gabas ta tsakiya face dai kasashen yankin ne kawai za su iya wannan aikin.
Babban kwamandan dakarun na IRGC ya bayyana hakan ne a matsayin mai da martani da kokarin Amurka na hada hadakar wasu kasashen duniya don abin da suka kira kokarin tabbatar da tsaron yankin Tekun Fasha musamman mashigar ruwar nan ta Hormuz lamarin da jami’an Iran da dama suka ce hakan ba lamari ne mai yiyu ba.
A kwanakin baya ne dai Amurkan ta kirayi wasu kasashen duniya wajen hada hadaka da nufin tabbatar da tsaron mashigar ta Hormuz lamarin da kasashe da dama suka yi watsi da shi da kuma kin karbar wannan goron gayyata na Amurka.
/129